Thursday, 1 May 2014
LABARAI
ci a Brunei
30 Aprilu 2014 An sabunta 10:59 GMT

Aika
Sarkin Brunei ya ce dokokin Allah ne, saboda haka ba za a bayyana su da cewa na rashin adalci ba
Sarkin Brunei ya kaddamar da shari'ar musulinci a kasar -- ciki har da hukuncin yanke hannu da jefe mutum idan ya yi laifi mai tsauri.
Sabuwar dokar dai ta fara aiki ne a wannan makon, kuma za ta hada da daure mutum ko cin tararsa idan ya aikata laifukan da suka hada da yin dabi'un da ba su dace ba da kin halartar sallar Juma'a.
Haka kuma za a yi hukuncin da ya hada da yin bulala da yanke hannu idan mutum ya yi sata, da kuma rajamu idan mutum ya yi zina ko luwadi da madigo.
Sarki Haji Hassanal Bolkiah yana daya daga cikin mafiya arziki a duniya, kuma ya ce dokokin Allah su suka fi dacewa da dan adam.
Masu kare hakkin dan adam sun soki lamirinsa
LABARAI
gano wasu karin 'yan matan Chibok hudu, da suka tsere daga hannun 'yan bindigar da suka sace su.
Patrick Abba Moro ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC, inda ya ce an gano daliban a garin Monguno dake jihar Borno a arewacin kasar.
Haka kuma ya kara jaddada kokarin da gwamnati ke yi, wajen ganin an ceto 'yan matan da aka sace sama da makonni biyu.
Iyaye da 'yan uwan 'yan matan dai sun nuna rashin jin dadi, game da rashin samun cikakken bayani kan abin da gwamnati ke yi kan batun
Subscribe to:
Posts (Atom)