Thursday, 1 May 2014

LABARAI

ci a Brunei 30 Aprilu 2014 An sabunta 10:59 GMT  Aika Sarkin Brunei ya ce dokokin Allah ne, saboda haka ba za a bayyana su da cewa na rashin adalci ba Sarkin Brunei ya kaddamar da shari'ar musulinci a kasar -- ciki har da hukuncin yanke hannu da jefe mutum idan ya yi laifi mai tsauri. Sabuwar dokar dai ta fara aiki ne a wannan makon, kuma za ta hada da daure mutum ko cin tararsa idan ya aikata laifukan da suka hada da yin dabi'un da ba su dace ba da kin halartar sallar Juma'a. Haka kuma za a yi hukuncin da ya hada da yin bulala da yanke hannu idan mutum ya yi sata, da kuma rajamu idan mutum ya yi zina ko luwadi da madigo. Sarki Haji Hassanal Bolkiah yana daya daga cikin mafiya arziki a duniya, kuma ya ce dokokin Allah su suka fi dacewa da dan adam. Masu kare hakkin dan adam sun soki lamirinsa

No comments:

Post a Comment